Advertisement

Ad code

Zafin Kai Hausa Novel Complete By Mamuhgee

 

Zafin Kai Hausa Novel Complete By Mamuhgee

Zafin Kai Hausa Novel Complete By Mamuhgee

Zafin Kai Page 1

Gyara tsayuwarta tayi ahankali tana sauke idanuwanta daga kallon dattijuwa kuma tsohuwar matar dake a kansu tsaye tana musu fada cikin Iko da bayyanarda rashin ruwanta da abunda zai biyo bayan kuskuren da sukayi a lokacin tareda yi musu tini da ukubar dake tafe mai zafi.

Ita din dake tsaye a kan nasu tana fadan mahaifiyace ga Wanda ya haifesu ma'ana mahaifinsu babansu kaman yanda mutane ke Kiran Wanda ya haifesu da sunan baba kuma uba,
Su bazasu kirasa da kalman babansu ba sbd shi din Wanda ya haifesu ne kawai bawai babansu ba kaman yanda kowane uban yake,

Sun banbanta kalman mahaifi da baba ne sbd basu tantance me UBA Kuma baba yake nufi ba a zahirin haqiqanin gaskia dan basu taba gani ba ko samun kauna,kulawa,tausayi,jin qai ko wata fuskar dake tabbatar musu da su ‘din ‘yayane masu baba uba kaman kowane ‘yaya na halak da wainda bana halak din ba.
Amma a zahiri kusan sune suka fi tantance kalman mahaifi da ake nufi da wanda ya haifeka sbd zallar girmamamman ikonsa na haihuwarsu tareda juya rayuwarsu yanda yaga dama a mafi wulaqantacciyar hanya da karshen rashin daraja da rashin amfani shine mafi babban lamarin rayuwar dasuka tabbatar a duniya Gameda kalman mahaifi a gurinsu.

Matar data haifi mahaifinsu a zahiri itama bazasu kirata da kakarsu ba kai tsaye sbd babu wata sanyayawa ko kaunar Jini datake bayyanar musu da kalmar kaka da Ake kira a duniyar tasu,

Mahaifiyarsu,uwarsu,Annensu,Farin cikinsu kwalli daya a duniya dasike tsananin so da kauna sun kasance bayi a tare ita wadda itace asalin bautar acikinsu sbd shekarun data debo tun kafin haihuwarsu tana rayuwar bautar a tsakanin ‘da da uwar a wulaqance sbd takalmin daya saka kudi ya siya ya taka sunfita daraja a gurinsa bare mahaifiyarsa datake ganin tabbas Annen batada amfani a rayuwarsu kwata kwata saima wulaqantacciyar lalurar data zame musu da tarin ‘yayan matan data haife musu a gidan babu wata daraja ko daya dasuka qaru da ita,

Bayan shekarun data debo cikin azaba da ukubar  uban nasu a yanzu gasu tareda ita cikin qangin bautar a tare,
Basuda yanci da ikon kansu sai yanda mahaifinsu yayi da raunanniyar rayuwarsu koda kuwa zaiyi gunduwa gunduwa da sassan jikinsu basa iya dago kai ko fuskarsa su kalla bare idanuwansa dan kuwa sunfi maraba da masifa kowace irice akan dago kai su kalli idanuwan mahaifin nasu domin garesu kaman aikata wani babban mummunan sabo ne dazai iya kaisu ga shiga masifar datafi ka kona kanka da tafasashen ruwan zafi.

Sumayya da datafi kowanne a cikin su hudun rauni sosai a hankali ta sake yin qasa da kanta muryarta Mai rauni na Dan rawa tace,

"Zamu sake gyarawa kafin ya dawo Amma Dan Allah hande ki taimaka a bawa Anne abincin kafin ya dawo…"

Katseta hande tayi hankali kwance cikin Dan fada sbd batason batawa kanta karfi da rai ko lokaci akan lamarinsu sbd tasu rayuwar tagama lalacewa dan haka bazata bata karfinta a banza ba akan abinda yake tamkar matacciyar rayuwa mai numfashi tace,

"Babu ruwana da taka dokarsa,
Ita Annen taku zatace bata Saba da yunwa bane tsowon shekaru ashirin da Dori da aurenta dashi?

Kuda kuke yayanta kunzo daga baya Kuka Saba da yunwar bare ita,

Idan zata ara jarumta ta ara tayi rayuwar yanda ta Saba ni banason janye janye,
Kuje ku jira ya dawo yagama ku samu abinda zaku samu kuci din bansan sabon salon da bansaba dashiba.

Dukkaninsu babu wanda ya dago kansu na qasa suna sauraren fadan nata babu mai ikon dazai iya dagowa ya qara ko kalma daya acikinsu.
Ajiyar zuciya Annen dake tsaye jere tare dasu kaman bayi tsaye gaban sarauniyarsu ta sake tareda sake yin qasa da kanta cikin girmamawa mai tsananin gaske ta bawa Uwar uban gidan nasu hakuri sbd kwata kwata ba miji bane ko uba kaman na kowa uban gidansu ne a yanda suke rayuwar.,
Shi kansa bai daukesuba bare ya taba kallonsu a matsayin mata da ‘yaya kallonsu yake tamkar wasu dabbobi ko bayi daya saka kudi ya siyo suka zama garke.

Babu abunda Hande tasake ce musu bare ta sake kallon inda suke saima maida hankalinta datayi Kan sakon datake dubawa cikin qaramar wayar hannunta da batama gane komai da aka rubuto din.

Dagowa Anne tayi ta kalli 'yayan nata ahankali cikin sanyin murya tace su tafi.

Babu Wanda jikinsa ba amace ba suka juya a jere kaman kashin awaki suki bi bayan mahaifiyar tasu kafafuwansu a sake ba qwari kaman taliyar hausa sbd yunwa da wahalar data Dade da ginuwa ta hade da Jini da gabban jikinsu.

****BENAZIR ce kawai me qwari da dauriya tareda karfin zuciya a cikinsu,
Sumayya da mahaifiyarsu nada rauni mai karfi da yawa Dan har gwara mahaifiyar tasu akan sumayya wadda ta kasance rauninta yayi yawan da kusan koyaushe ta tsaya gaban mahaifinsu numfashinta Neman fita kirjinta yakeyi sbd tsoronsa daya dasa musu tun suna qananunsu har zuwa yanzu,

Mahaifinsu tamkar wani dodon tsawa ne a rayuwarsu,
Bai taba barin tsoronsa da shakkarsa sun girgiza daga zuciyoyinsu Koda second dayaba sbd tsananin azabarsa da mummunan horonsa garesu,
A duk lokacinda amon muryarsa ya sauka kunnuwansu Gangar jikinsu da zuciyoyinsu shiga rawa  da mafi girman firgici sukeyi tareda tsananin tsoro da tashin hankali mai girgiza hankali da nutsuwa,

Shi din kaman wata tsawa da walkiyar data gurbata rayuwarsu ne ta lalata musu,
Tamkar wulaqantaccin bayi da basuda daraja suke a karkashinsa,
Tufafinsa,talarmin sawarsa da dabbobinsa sunfisu daraja a gabansa sbd dabbobinsa yana musu kallon kadarar kudi ne dazai qaru dasu sabanin su dayake kallon wahala ce kawai da rashin amfani a gabansa,

Almajirai dake cikin bola suna yawo sunfisu yanci da gata sbd su din Sunada ikon daga kansu su kalli abunda sukeson kalla tareda ikon zuwa ko karban sadaka daga duk wanda suke so Amma su daga lokacinda mahaifin nasu ya wanzu a guri numfashi mai karfi basuda iko ko yancin yi batareda shine ya bada damar ba bare motsi Mai karfi saida izininsa,

Mahaifiyarsu ta share shekaru da aurensa cikin ukuba da azabar data cinye lafiyar kwakwalwar kanta da gangar jikinta harma da ganinta,

Ta haifesu su hudu duka mata cikin azaba da wahala,
Ra rena cikinsu su duka hudun a mafi wahalallan hali da kadaici da yunwa da ciwo rashin daraja,

Haihuwarsu ta ninka azabarta,quncinta,yunwarta da rashin darajarta,
Yawansu ya ninka azabarsu suma tun zuwansu duniya,
A duk lokacinda dayansu ya qaru a duniya sai sauran sunyi kukan qaruwar azabarsu,
Azabar datayi sanadin rasuwar daya daga cikinsu,

Duka wannan tsana da azabar akan suna 'YAYA MATA ne,

Tsanar dayakewa Yaya mata ne kokuwa kaddararsa ce yasa Allah ya jarabcesa da haihuwarsu su hudu duka yaya matan?

Meye laifinsu?
Meye illarsu?
Meye illar samunsu dazai Rainesu tamkar dabbobin daya tsinto a daji.

Sun kasance tamkar mujiyoyi a cikin alumma sbd horon dasuka taso acikinsa hannun mahaifinsu da mahaifiyarsa yasa suke kallon kansu tamkar wasu halittun da kadan ne sukafi dabbobi daraja a cikin mutane.

Mahaifiyarsu ta rasa cikkakiyar lafiyar kwakwalwar kanta tun suna qananunsu,
Girmansu yasa tadawo kaman daidai sbd azabarta ta ragu anraba mata itada 'yayanta,

Abincin dasukeci agidan suna samun cinsa ne bayan Mahaifinsu da mahaifiyarsa sunci sun rage Kuma Sunada iko da daman cinsa ne a gurinda zasu wanke kayan da aka Gama cin abincin dukkaninsu a kwano daya,.

Menene ci a koshi?
Wannan kalma ce da basu taba sanintaba Dan bata taba faruwa dasuba tsawon rayuwarsu,

Hutu, Shima wani Abu ne da basusan dashiba sbd babu shi a abunda suke samu.

Bauta,
Wahala,
Yunwa,
Azaba, sune abubuwan dasukafi sabo dasu,

Ribarsu biyu dasuke gani sun samu a rayuwarsu shine ibadarsu da kaunar junansu dasuke tsananin yi..

SUMAYYAH itace babba a haihuwa,sai SAMIRAHwadda tazarar shekara biyu ne rak a tsakaninsu,
sai BENAZIR wadda itama shekara daya da watanni ce tsakaninta da Safnah sai SAFNAH wadda itace qaramarsu itama shekarun dake tsakaninta da benazir biyu ne sbd yanda ako wane lokaci mahaifin nasu yake zuwarwa mahaifiyar tasu ba tsari ba kulawa ba komai,

Bai taba shaawar qarin aure ko neman wata matar banzar ba a waje sbd tsarinsa da tsananin so da kaunar abin duniya dake ransa,

Neman mata ko caca ko sunansu baa fada a gabansa sbd tsananin son kudinsa da bazai iya hakuri ko tinanin ma rasa ficika ba aciki yasa bai taba shaawa ko kallon inda ake caca ko zina ba.

Asalin tsanar Bena a ransa tafi ta kowa acikinsu ta musamman ce sbd cikinta ne ya cinye Rabin arzikinsa dayake ganin wata mummunar kaddara ce garesa zuwanta duniyama gabaki daya bayan haihuwarta sabanin duban da likita yayi masa akan namiji ne acikin,

Bai taba son wani Abu a duniyaba kaman yanda yaso cikinta,
Allah ya jarabcesa da son cikinta
So me tsananin dayasa ya kashe dukkanin tattalinsa akan cikin Wanda akan cikin yafara Kai matar tasa asibiti sbd ko uwarsa data haifesa duk ciwo Bai taba kaita asibiti ba sai akan wannan cikin
Daga karshe dukkanin burinsa da muradinsa ya lalace a kan idonsa da aka sake iso masa da sakon 'ya mace aka haifa wadda tun a asibitin yaji tsanarta fiyeda uwar da sauran yayan da Ake haifar masa haka zalika tunda ta fado duniya bai taba daukanta a hannunsa ba haka bayajin zaiyi har abada kuma daga kanta bai sake ko kallon abinda matarsa tasa ta haifa.

Tsanar dayake wa Benazir ta bata qarfin zuciya fiyeda Yan uwanta dakejin radadi da raunin tsanar da Mahaifinsu ke musu sai dai dukkanin su basusan me kaddararsu ta tanadar musu ba a gaba dagasu har shi mahaifin nasu.

****Dakinsu suka shiga kowannensu ya nema guri ya zauna a hankali Banda safnah data tsaya daga bakin window Idanuwanta da sukai ciki sbd rashin kuzari tana kallon bayan gidansu a jikin windon jikinta na qarasa sanyi zuciyarta a ko yaushe babu abunda take tinani sai yanda rayuwa ba'a karkashin mahaifinsu ba zata kasance,

Shin sauran 'yaya ya sukejin mahaifansu acikin ransu?
Da wani ahalin aka haifesu koda a matsayin ‘yayan shegu ne zasufi farin ciki da nutsuwa,
Meyesa basu zamto cikin yayan da ake haihuwarsu ana jefarwa ba sunfi kwanciyar hankali koda talaka ne ya tsincesu zaifi musu akan wanda suke karkashinsa a matsayin mahaifi yanzu,

A koyaushe burinta shin da gaske akwai wainda ke siyan mutane suyi bayi dasu kaman yanda mahaifin nasu keda tsananin buri da fatan Ina zai samu masu siyan bayi ya saida dukkaninsu Koda a farashi mara daraja ne a tafi dasu ya huta da ganinsu shima a rayuwarsa,

Idan da gaske akwai irinsu to tabbas itama tanason ta kasance a siyeta a tafi da ita tabar mahaifinsu da sunansa kawai aka kira dukkaninsu zuciyoyinsu tsalle sukeyi cikin tsoro Mai girma da firgici Wanda wani babban balain ne ma bayyanarda rawar jikin tsoronka a gabansa wannan ma wani nauyin horon azabar ne dasu kadai sukasan wutar tsoro da rawar dake gudana a jininsu gurin boye hakan.

Ahankali hawayenta suke gangaro
duk tsanani hawayensu ma basuda yancin gangarowa a gidan saidai idan sun shigo dakinsu su iya sakinsu,

Ahankali cikin muryarta datake bayyanarda rauni da qulafucinta akan rabuwa da rayuwar datake ciki tace,

"Allah yakawo kaddarar dazata rabamu da gidan nan Koda ta wahala ce.

Dukkaninsu sun ji abunda ta fada cikin raunin
Sun Saba jin hakan daga bakinta sbd a cikinsu itace tafi kowa raunin son tafiya tabar gidan Koda zata tadda rayuwar wahalar datafi ta gidan,

Duk tsanani sun San bazasu taba barinta kwatanta guduwa ba kaman yanda itama bazata taba kwatanta guduwarba sbd azabar kwatanta guduwar ne yayi sanadin rasuwar SAMIRAH wadda ta rasu rasuwa Mafi Karya zuciyoyinsu.

Zafin Kai page 2

Samirah ta rasu ne bayan da azabar tayi masu yawa ta girmi tinani da dauriyarsu harma da duk jarumtar da suke tinanin sunada ita,

Cikin tsakiyar dare guraren karfe uku na dare ta fita dan guduwa bayan ta tabbatarda a lokacin bacci mai karfi yake daukan Ababa sbd yawanci yana kaiwa karfe daya koma harda mintina kafin yayi bacci sbd babu daren da baya lissafin dan arzikinsa da kuma lissafin yanda zaiyi da rayuwarsu kota hanyar siyarwa kota hanyar samun masu kudin da suka amsa sunan asalin masu kudi su auresu koda a matsayin matan biyan buqata ne kawai shi dai idan zasu fita rayuwarsa amma a dayan bangaren tinaninsa shine karatun daya sakasu sbd idan har bai fanshe komai nasa a gurin masu fataucinsu ba to tabbas dole idan masu dollars ne zasu auresu kota tsiya yasan dole ana buqatan ilimin boko da 'yar wayewar ilimin a tare dasu kafin su shige.

A daren kwanon abinci daya suka samu su dukansu wanda dukkaninsu loma bibbiyu sukai suka barwa mahaifiyarsu sauran sbd karfinta na shekaru da wahala ta cinye,
A cikinsu yanzu Annen tasu ta zama tamkar itace qaramar kanwarsu gabaki daya sbd kowannensu tausayinta yake ji fiyeda junansu,
Tafi su gazawa,
Tafisu jigata hakama tafisu buqatan abinci a koda yaushe aka basu din sbd rauninta.

Samirah a cikinsu ta kasance batai jin qan sauran ba sbd a koda yaushe indai zasuyiwa 'dayansu sacrifice na wani abun itace take kasawa shiyasa koyaushe batada burin guduwa daga wannan rayuwar mai kama data fataucin bayi,
Burin guduwa da tserewa mahaifinsu yasa abin ya zauna a ranta har kusan ta shafawa Safnah kwadayin guduwa daga wannan masifar dasuke kira da rayuwar gidan ubansu.

Yunwa,azabar zafi data sauro daya zama tamkar bugun numfashinsu sbd babu yanda zaayi su kwana su tashi batareda sauro fiyeda dari a dakinsuba sakamakon rashin kofa sai labule windon dakinma kusan dan kada su gudun ne ko barayi su shigo ta nan su masa sata a gidan yasa ya saka musu sbd yana ta bayan gidan ne windon.

Tashi zaune samirah tayi ahankali daga kwancen datake gefen mahaifiyarsu akan babbar tabarmarsu dasuke kwana zube akai kaman an shanya su,

Annenta ta zubawa ido Ahankali jikinta na mutuwa tareda karayar zuciya da tsananin kaunarta da tausayinta na yanda zataji a matsayinta na uwa idan aka wayi gari babuta ta bata ta shiga duniyar da Anne da yan uwanta basu saniba ko zasu sake haduwa har abada,

Hawaye masu zafi ne suka gangaro mata sbd tinanin azabar da zasu iya sha daga mahaifin nasu akan guduwarta saidai bazata iya zama a cikin wannan rayuwar ba sbd tsoron dake zukatansu wadda mahaifinsu ya saka musu kawai zata iya kashesu kokuma su qare da juyayyar qwaqwalwa kaman mahaifiyarsu wadda ta zama ita da qaramin yaro wani lokacin banbancin kadan ne.

Hannuwanta ta daga Ahankali ta kallo tafin hannuwanta dake a cabe suna wani irin ruwa sbd azabar ruwan zafin da akai mata a jiya
Ta tabbatarda zata rube a hakan a yanke hannuwan kokuma ta warke amma bazaa taba kallonta a nuna an mata hukuncin ba bare a neman mata magani,

Zata gudu tabar gida koda yan uwanta da Annensu zasu samu ragin mutum daya abincinda ake basu ya dan qara yawa a cikinsu sbd tasani har abada idan har a gidan zasuyi rayuwa bazasu taba cin abincin da zasu qoshiba,
Qin da Ababa yayi musu zuwa gaba lokaci yakuma ja yaga baida mafita komaima zai iyayi dan ya kawai dasu daga gabansa ciki kuwa zata iya cewa harda kashewa dan karfin ransa da taurinsa babu kowane kalar tausayi ko imani acikinsa,
Abu daya ke karyar da taurin ransa da girmansa shine kudi,
Bai hada komai da dukiyarsa ba wadda idan ana maganar masu dukiya baya cikin layi ko kusa amma kaman yanda yake fada kowa da nasa yake tinkaho,
Baya roko,baya daukan reni a gurin kowa sbd a ganinsa babu mai kudin da zai iya basa irin kudin dayakeso sbd shi a gurinsa masu lissafi da dollers din America sune masu kudin gaske dasuke isa su fada ya saurara.

Bin 'yan uwanta tayi da kallo daya bayan daya hawayenta na sake gangarowa da dumi mai zafi tana sake kallon yanda kowannensu yake fidda wahalallen numfashin dake fitowa daqyar sbd yunwa amma a hakan suke bacci kaman jarirai da basusan matsalar komaiba tsaban tawakalli da rungumar rayuwar da Allah ya jarabcesu da ita.

Kan benazir da zatafi kowa daukan wahalarsa ta tsaida idanuwanta tana jin tausayinta sbd azabarta tafi ta kowannensu akoda yaushe amma Allah zai duba lamarinta da sauran yan uwan da mahaifiyarsu wadda guduwanta saiya taba Annen sosai.

Hannuwanta masu tsananin azabar ta dafa tana rintse ido sbd radadin dayake ratsata ta miqe tsaye tana sakawa zuciyarta karfi da juriya ta janyo qaton mayafin Anne dayake gefe aje ta yafa ajikinta ko takarmi bata sakaba sbd zaiyiwa yan uwanta amfani idan wani ya rasa na sakawa yayi amfani da nata din.

Kofar ficewa ta nufa batareda ta waiwayoba sbd raunin da zuciyarta keyi idan tana kallonsu,

Safnah data ji motsinta kadan ta bude idanuwanta tana kallonta batareda ta motsaba idanuwanta itama sina cikowa da hawayen tausayin Annensu da yan uwanta dazasu bari dan kuwa matuqar taji samirah din ta fice batareda matsalar komaiba to itama miqewa zatayi tabi bayanta su tsira tare.

Ahankali samirah ta ringa daga qafafunta dake rawar tsananin tsoro da bugawar zuciya mai karfi ta nufi hanyar dazata kaita kofar dakin Hande wadda mukullin qaton padlock din gidan yake hannunta bayan sakata kusan biyar dake jikin kofar shigowa gidan.

Cikin sanda tana dan rintse idon azaban hannunta dayake ruwa sosai ta isa dakin ta tura kofar a hankali tana zira kanta kadan taga handen tayi nisa a bacci sosai kan qatuwar katifarta mai taushi da tudu.

Cikon sanda ta isa inda tasan mukullan na gurin ta saka hannunta mai ciwo ta riqo mukullan ta  damqo a hannunta ta matse sbd kar suyi qara su tada Handen
Tanaji azabar yanda ta damqesu a hannunta dayake a cabe tana ratsa zuciyarta har cikin kanta amma ta daure.

Tana numfashi da qyar ta fito daga dakin ta tsaya tsakar gidan ta saki wani wahalallan numfashi mai dumi da azaba hawayenta na kasa gangarowa daga idanuwanta dasukai ja.

Safnah dake rabe bakin kofa daga cikin dakinsu tana hango samirah din taga komai ya tafi daidai ta fito sake tsayuwa tayi daga cikin dakin tana dan sake ziro kanta kadan dan kafarta bazata sako tsakar gidanba dan hakan kawai zai iya sakata rasa qafafunta idan Ababa ya kamasu gashi tana ganin dakin Hande da samirah din ta bari a bude wanda iska da sanyi zai iya farkar da ita taganta amma bazata iya fitowa tace mata ta rufe dakinba dan ta zabi ta boye kanta ga wannan aikin dayake sunan siradin tsira kona halaka.

Kofa samirah ta nufa jikinta na rawa sosai sbd hannuwanta dasuka kasa riqe mukullan da kyau,
Hannu na wata irin rawa ta kamo katon padlock din dayafi karfin hannunta ta saka key din daqyar amma ta kasa saka karfi ta murda ya bude sbd hannuwanta dake jini gabaki daya wutar takoma mata sabuwa gashi  duka hannuwan biyu,

Ninka tashi hankalinta yayi tareda wani irin firgitaccen tsoro dataji yana shigarta mai karfi a lokacin sbd kaddararren aikin tsautsayine da babu komawa baya sbd tariga ta barko barnar tunda ta sato mukullin gwara duk tsanani ta balle ta gudu akan Ababa ya risketa tabbas hannuwanta bazasu qara moruwaba kuma.

Yanda jikinta ke rawa yana jijjigar tsoro da firgici tareda tashin hankali mara misali yasata kofar da padlock da mukullan suka fara bada sauti mai karfi,

Safnah dake labe wata irin rawa qafafunta suka dauka  zufa na tsiyayo musu a ciki zuciyarta ta hau bugawa da tsalle kaman zata fado sbd tasan komai ya lalace.

Hande da iska tareda sanyi sukai mata yawa cikin bacci sbd kusan acan suke qarshen gari anguwar da babu mutane da yawa dan sam Ababan baya kaunar zama cikin mutane sosai sbd baya kaunar ko so daya ashiga huruminsa da rayuwarsa da wainda ke karkashinsa.

Bude idanuwa Hande tayi sai kawai tayi ido biyu da hasken taurari kofarta a bude,

Bude ido tayi da kyau tana kokarin tashi zaune sbd ta tabbatarda ta rufe kofar dakinta duk tsanani bata bacci daki a bude.

Motsin bude kofar gidan dataji ne yasata tasowa ahankali tana leqowa cikin tsoro da fargabar wane tsautsayin ne ya kawo barawo gidan dan kuwa Ababa tsaf zai harbesa da bindigarsa ta mafarauta.

Zafin Kai page 3

Sam Hande bata wani tsoro kaman ‘dan nata take duk shi kam na musamman ne a fagen taurin zuciyar da batada tausayi ko taushi ko kadan akan komai da kowa sai akan qaruwarsa,dan haka kai tsaye hande ta fito tsakar gidan idanuwanta a kofa tana qwala kiran Ababa din da karfi sbd ya fito cikin sauri da shirin harbe kafar koma wane shegen ne ya shigo musu gidan…..bakinta kasa qarasa magana yayi lokacinda ta haske kofar da fitilarta me tsananin haske taga samirah dake dukan kofar cikin tashin hankali da neman mutuwa ta dauketa a lokacin idan bazata zamu kubutar tserewaba a daidai wannan mummunan lokacin.

Cikin sauri idanuwa a rufe Ababa din ya fito yana saita doguwar bindigarsa da kofar ba wata wata ya harba da karfi ko ita handen bai tsaya cewa ta matsa daga gurinba saida qarar bindigar yasata zubewa qasa sbd babu abinda yake rabata da nutsuwarta da hankalinta ita kuma sai bindiga sanin aikinta ba wasa lahira take.

Safnah dake daki tun fitowar hande daga daki ta yanke jiki a gurin ta zube sbd mummunan tsoro da firgici mara misalin daya tsayar da bugun zuciyarta duk da ita a daki take boye dan haka kwatanta halinda samirah take ciki zaiyi wuya sbd fitowar mahaifinsu kafin ya harba bindingar zuciyarta ta tsaya cak qafafunta suka sare dan haka koda ya harba bindigar kofar gidan yayiwa mummunar fasawa sbd bullet dinta na fulogon mashin ne.

Cikin wani irin firgitaccen tsoro dukkaninsu dakin suka farka suna tashi zaune idanuwansu na rarrabuwa akan junansu sbd duk irin haka tafari junansu suke fara tabbatarda suna tare guri daya saisu nutsu basa fitowa matuqar ba cewa yayi su fito ba.

Benazir ce tafara bude baki tana rarraba idanuwanta dake wartsakewa daga bacci cikin tashin hankali da tsoro tace,

“Samirah,ina samirah?

Dukkaninsu sai alokacin suka miqe tsaye cikin rawar jiki da tashin hankalin dayake neman fin karfin bugawar zuciyarsu suna rarraba idon neman samirah din
Sumayyah kuwa kan safnah dake zube tana qanqamewar tsoro da daukewar numfashi tafara girgizata da karfi tana tambayarta ina samirah amma sam safnah bata iya motsi bare fahimtar me sumayya ke fada bare ta iya bada amsa.

Cikin wani irin karaji mai karfi da firgitarwa daya saba kada hanjin cikinsu dashi a zafafe da wani irin fushi da zafin dayake ci cikin kansa yace,

“Guduwa zakiyi?
Ina zaki?
Kin san me kika aikata?
Kinada inda zaki iya guduwane ki tseremun?

Shaqota yayi da wani irin karfi da zafi ya buga kanta da jikin kofar yana take qafafunta da nasa da karaji ya kira sunan Hande yace ina ta samu mukullan bude gidan?

Kallonta hande tayi cikin baqin ciki da takaicin tado musu da hauka da tashin hankalin Ababan ta miqe tsaye daga zubewar datayi rai bace tace,

“Nawa ne ta sato harda barmin daki a bude”.

Wani sabon gigitaccen marin bayan hannu ya sakar mata wanda ya sata zubewa qasa bakinta na tsiyayar jini sakamakon hakorinta ‘daya da ya fita take sbd tsananin zafi da radadin marin.

Damqota yayi ya dago sama ya sake sakar mata wasu mahaukatan marikan guda biyu dasuka dauke dukkanin wutar jikinta ta silale a gurin take ya take hannuwanta dake jini da ruwa a fusace yasake maimaita mata tambayarsa daidai nan su Benazir dasuka fice hayyacinsu suka fito zuciyoyinsu suna rawa da tsallen munannen tsoro saidai dukkaninsu babu wanda ya iya daga kai ya kalli abinda Ababan kewa Samirah saima hana tashin hankalinsu bayyana sukai sbd hakan kaman wani laifin ne.

Anne dake kusa da benazir qasa daukanta kafafunta ke kokarin yi amma benazir ta riqeta tana kokarin hanata bayyanarda masifar dake ragargaza zuciyarta akan ‘yarta datake kallo ana hallakawa amma babu abinda zata iyayi ko ikon dagowa ta kalla batada dashi dan haka takejin kaman ana zare naman jikinta ne daga qashinta,
Sumayyah da rauninta baya dauka tini ta zube qasa da rarrafe cikin tashin hankali da ficewa hayyaci ta koma dakinsu ta zube kusada safnah da har lokacin bata dawo daidaiba jikinta kerma yakeyi duk da babu qarar ihu ko kuka ko kadan dayake tashi sbd azabar datayiwa samirah din yawa gakuma daman horan daya musu duk tsananin azaba basa masa ihu ko kuka dan haka suka taso da iya riqe ciwo a zuciya da ciki.

Benazir ce kawai a tsaye kanta a qasa harya gama yiwa samirah din dukan mutuwa wanda ko hannunta bata iya motsawa bare wani sassan na jikinta,

Juyawa yayi yabar gurin batareda yace komaiba ya shige dakinsa hande ma juyawa tayi tana haska benazir da fitila tace,

“Jata ki maidata daki idan tanada rabo zata shiga hankalinta idan ta warke”
Dakinta ta shige itama ta rufo kofa .

Sarewa qafafun BENAZIR sukayi ta zube a gurin tareda fashewa da wani irin kuka mara sauti ko kadan jikinta na rawa da qyar ta kai kanta gurin samirah din ta janyota jikinta tana sarewa da jini da numfashin da samirahn bata iya ja.

Samirah dake jin BENAZIR din sama sama hannu takeson dagawa ta taba Benazir din amma takasa sbd numfashin datake neman ja amma kirjinta baya karba.

Anne da kanta ta tako tazo hannuwanta na rawa ta kamawa BENAZIR sukai ciki da samirah din wadda numfashinta ya fara daukewa yana dawowa.

Kwantar da ita sukayi kowannensu ya zube gabanta babu mai iya cewa komai sbd basa hayyacin magana,

Sai alokacin safnah da sumayya suka fashe da wani irin kuka mai ciwo da radadi ba sauti,
Anne hawayenta bushewa sukai bayan ido data zubawa samirah din babu abinda take iyawa,

Benazir ma datake da jarumtar batada iyawa bayan hawayenta dake gangara da gudu masu tsananin zafi.

Haka suka zuba mata ido bayan jinin dasuka goge mata a jiki da ruwan zafi komai basida nayi mata dan haka suka ringa binta da addua har gari ya waye.

Koda safiya tayi gabaki dayanta ta kimbura sbd duka,
Kamanninta kuwa gabaki daya sun sauya sbd fuskarta data tashi daga fuskar kuruciya zuwa wani abun tsoron.

Karfe tara ya fito daga dakinsa kai tsaye ya tarasu ya tabbatar musu da babu wanda zai bawa samirah din kowace irin kulawa ta musamman kaman yanda tayi niyar tserewa da kanta haka zata miqe da kanta ta karbi hukincin daya yanke akanta na maidata dakin dabbobinsu acikinsu zata zauna har ranarda sanadin rabuwarsa da ita yazo maana idan ya samu gurin miqata tareda horon ko kofar gida bazata sake kallaba idan ta kalla saiya zuba mata maganin dabbobi acikin idanuwan dan idan ta makance ne kawai zata cire rai daga sake tinani.

Dakin dabbobinsa aka maidata  kusan zannuwansu suka hada sukai mata shimfida dashi tareda na lullubawa aka kwantar da ita har lokacin bata iya tayar da kanta saidai mumfashinta daya ‘dan daidaita.

Basuda ikon tsayawa kula da ita matuqar ba sun gama aikin dayake kansu bane dan haka ita kadai suka bari a tsakiyar dabbonin suka dawo zuciyoyinsu ba kuzari ko kadan.

Bangaren dabbobin kaman yanda suka saba shi suka fara dashi ta hanyar kwashe kashinsu tas da hannayensu suka share babban gurin tarefa tsaftacesa suka kwasa suka fitar tareda jerewa a dakin dayake tara takin kashin.

Daganan aikin cikin gidan sukai tareda wankin kayansa dana Hande da kullum sai anyi,
Aikin abinci suke gamawa da wuri kafin su koma aikin kulawa da dabbobinsa,

Basuda hutu ko kadan tunda suka kammala karatun secondary din gwamnati wadda nisanta ma da abin hawa 700 ake zuwa a dawo 700 amma ahaka suke zuwa da qafa su dawo da qafa ba karin kumallo ba ruwa haka yayi musu mummunan horon da sam basa iya zama ko muamala da mutane,
Tamkar mujiyoyi suke acikin mutane har sukai suka gama babu wanda zaice daya daga cikinsu tayi muamala dashi kota gaisuwa saidai idan ka gaishesu su amsa kokuma sallama ita sunayi,

Koda suka kammala babu wadda taqara sanin meyake wakana a duniyar wajen gidan dan kuwa ya rufesu babu inda suke zuwa sbd killace sirrin rayuwar gidansa,

Sam baya tsoro ko shakkar kowa baya shayin fadar maganarsa kai tsaye ga duk wanda yakesan fadawa,
Baa shiga huruminsa ko kadan kaman yanda baya shiga na kowa dan kuwa ya kame kansa ga lamarin kowa abinda ya shafesa yake gabansa kawai yakeyi,

Masifaffe ne,
azababbe ne,
Mara tausayi ne,
Mara shakka ne,
Mayen dollar da naira ne uwarsa data haifesa baza iya cin sisinsa idan ba na ciyarwar datake ci a gidanba,
Tsananin so da qulafucinsa akan kudi yasa su kansa yayan bai yarda ya koresu ya rasasu ba a banza ba batareda ya ci ribar ciyarwar da zaman dayayi mahaifi a garesu,
A karshen buqatarsa duk munin aiki ko sanaar mai kudi zai basa aurensu shiyasa ya danne zuciyarsa ya basu karatu da ilimi ba sbd burinsa na fanshe wahalarsa akansu babba ne.

******duk saurin dasukai na kammala tarin ayyikan bautar dasuka saba basu samu dawowa ga samirah din ba da wuri Anne ce kawai a kanta
Zazzabi mai qarfi ha riga ya rufeta haka zalika raunikanta sunyi munin kallo haka suka sake wanke mata suka gyarata aka sake kwantar da ita.

Abincin da aka basu duk yanda sukaso yashiga cikinta ba dama tunda ba ruwa bane,
Sunaji suna gani ahaka suka ringa jinyar samirah din wadda kusan kaman rubuwa ne hannuwanta sukai sbd wasu irin ruwa da wari mara dadi dasuke fiddawa duk da wanke mata da sukeyi kullum,

Tana iya magana amma a hankali amma bata ita tashi zaune sbd kaman harda bayanta ya samu matsala dan haka haka suka ringa jinyarta cikin sarewa da addua har tsawon sati biyu harta fara warkewa hannuwan ne kawai da rashin tashin sai gashi Kwatsam Allah ya karbi ranta da tsakar dare bayan sunsha kukan alamar tafiya dasuka gani a tareda,

“Mutuwa batada magani tafiya dole ce” itace kalmar data fada a lokacinda takeji itama tafiyar zatayi tabar uwa da yan uwanta a halinda basusan su yaya nasu qarshen zaizoba.

Tayi kuka  acikin yan uwanta sosai a raunane sbd tausayin kanta dana mahaifiyarsu da nasu fatanta duk tsanani duk wuya su kasance a tare babu ‘baraka.

*****Rasuwar samirah ya sake taba Annensu sosai haka suma dan kuwa rayuwa taqara tsanani da qunci sbd a zahiri Ababa yace yafara gano asarar dasuke neman ja masa tinda samirah ta bude musu hanyar tinanin guduwa dan haka ya tsananta musu fiyeda shekarun dasuka debo,
Ya zaburar da zuciyoyinsu gabaki daya basada wani motsi da zasuyi batareda tsoro da shakkarsa suna firgatasu ba dan haka ko a mafarki babu wanda ya yarda yayi mafarkin tinanin gudawa,
Zasu zauna tareda mahaifiyarsu wadda ya kafeta daga ranar daya aureta ta yanda bazata taba tafiyaba ko ina har abada sai mutuwa dan haka suma zasu zauna tareda ita har sai yanda Allah yayi dasu din su duka.

Wannan tinanin Benazir datafi kowa tsananin so da kaunar Annensu ne da sumayya amma banda safnah wadda a yanda komai na rayuwarsu ya qara tsanani da qunci tana nan da burin tseratar da kanta daga wannan rayuwar da basuda tabbacin fita ko Rashin fita har abada.

Zafin Kai Page 4

Rasuwar samirah ya taba Annensu sosai fiyeda yanda suka saba hadiye kowane irin yanayi dazai riskesu
Qwaqwalwanta ya sake tabuwa sosai dan haka kusan koda yaushe tana daki a zaune zugum bata komai haka take wuni haka suke kwana da ita,

Sumayyah ma rasuwar ta girgizata tareda firgitata sosai itada safnah ta yanda a yanzu amon muryarsa kawai dukkaninsu fitar dasu hayyacinsu yake jikinsu ya shiga rawar tashin hankali.

Biyayyarsu ta ninku fiyeda baya,
Tsoronsu ya qaru fiyeda baya,
So da kaunar junansu ya karu a zukatansu fiyeda baya haka zalika tausayi da kulawan mahaifiyarsu da suka duqufa yiwa adduar samun sassaucin tabin kan nata sbd qarasa juyewar qwaqwalwanta na nufin Ababa zai iya miqata ga titi ta qarasa haukacewa acan wanda sukuma a yanda sukeji rabuwa da mahaifiyarsu kaman abu ne da mutuwace kawai zata rabasu.

Safnah a yanxu da komai yayi tsanani bata tinanin kowa da komai face kanta,
Mafita take nemarwa kanta koda ta mutuwar ce itama tabi samirah ta huta…

Lokacin rasuwar yaja sosai addua da kulawar dasukewa maihaifiyarsu yasa ta dan dawo daidai lokuta da dama a hankalinta take duk da hakan kusan gabaki daya Ababa yasa dokar karta fito ta ringa zama a daki sbd idan yana ganin yanayinta zai iya kaita gidan mahaukata idan akwai.

Jin hakan yasa suke killaceta a daki sam basa barinta fitowa idan ba bandaki ko alwala zatayiba,

Sauki na samuwarta sosai Hande tasa tadawo Ayyukan da aka saba da ita na wahalar.

Bai taba yarda da kowaba a rayuwarsa bayan kansa
Hande data haifesa bata taba sanin komai daya danganci samu ko dukiyarsaba,
A koda yaushe sune suke masa lissafi a gabansa tas sbd sunada kokari akan ilimin da suka dan samu daga karatun da sikai.

Sun rungumi kaddara sun rungumi rayuwar dasuke ciki sbd suna kiyaye komai girman doka da umarninsa da dukkanin imaninsu,

Abu daya ne yake girgiza jarumta da zuciyar Benazir shine duk lolacinda safnah ta furta kalmar barin gida sai taji zuciyar ta wani irin nauyi da faduwa,
Ba iya damuwa da tsoron abinda zai iya faruwa da safnah din bane idan Ababa ya kamata kaman yanda yakama samirah koma dai menene tasan ba lallai akwai alkhairi tattare da hakan bane.

Dukkanin halaye dake bayyanarda boyayyan son iya kai dake zuciya da jinin safnah yana bayyana ne tun data busar da zuciyarta ga son tserewa kota halin yaya tabar gidan.

********a shekaru yanzu bazasu wuce sha bakwai zuwa sha takwas ba sumayya ce mai sha tara zuwa ashirin,
Dukkaninsu kyawawa ne duk da kasancewarsu ba masu hasken fata ba sosai,
Mahaifiyarsu Anne marainiya ce da Ababa din yayi shaawar aurenta sbd batada kowa batada mai tsaya mata a duk rayuwar da yayi niyar yi da ita,
Batada uwa bata uba sai kakarta bara sukeyi ya aureta ko wata baa rufa da aurenba kakarta ta rasu ya tattara ya baro garinsu da ita da mahaifiyarsa ya dawo birni ya dasa sabuwar rayuwarsa anan inda yake sanaar dabbobi da kasuwancin babban shagon fata da kuma yawon kai manyan shanu da raguna garuruwa,

Bazaa kirasa mai kudi ba hakama bazaa kirasa talaka ba sbd cinsa da shansa da buqatunsa basufi karfinsaba,
Dukkanin masu aiki a karkashinsa basa jin dadinsa sbd mutum ne mara yarda da rashin daukar asara komai kankantarta baya dauka,

Baya shiga harkar kowa ba ruwansa da duk abinda zakayi koda mutum zaka kashe a gabansa zai iya wucewa bai shiga aikinka ba sbd duk duniya ya tsani a shiga nasa lamarin,

Tunda ya ware kansa daga anguwar dakeda mutane sosai ya dawo irin anguwannin karshe karshen gari inda babu mutane sosai ya kafa iyalansa da rayuwarsa harkokinsa kawai yakeyi,
Babu wanda yasan irin munanniyar rayuwar datake gudana acikin gidansa sbd basa zuwa gidan kowa kaman yanda bayason ana zuwa gidansa idan ba qaruwa yakeyi da kai ba,

Duk tsananim azaba da ukubar da yayansa suke ciki jikinsu baya nunawa sosai sbd kyan fatarsu dakuma fitar da basayi suna killace a gida kullum sai hakan yasa fatarsu take kaman a fresh haka zalika sunada jiki mai kyau,

Baida wanda ya tsana ya bude ido a duniya yagani kamar ‘yayan nan hudu mata da Allah ya basa,

Duk wani tinanin mafita akan yanda zaiyi dasu yayi sbd yanda ciyar dasu kawai kecin wani dan bangare na arzikinsa,
Idan baya qaruwa da kai sam bakada wani amfani ko darajar da zaiyi muaamala dakai,
Komai nasa akan lissafin qaruwa yake,

Anne wadda asalin sunanta yake banazir ita nata amfanin dan yana biyan buqatunsa na aure ne akanta shiyasa baya neman yanda zaiyi da ita din amma a yanda hauka ke neman shigarta daga ranarda ta tabbata ta haukace bazai barta ta qara kwana daya ba a gidansa bakuma tareda ‘yayanta zata tafi ba dan su lissafinsa akansu mai girma ne saiya fanshe komai nasa dasukaci tsaf da yardar Allah.

Dukkaninsu bayan sumayyah datake ta farko babu wanda shine ya rada masa suna a cikinsu
Hande ce take rada musu suna
Benazir kuwa sbd tsanarta datafi ta kowa ita kanta Hande kasa saka mata sunan tayi shiyasa Annen ta mayarwa ‘yar da sunanta ta saka mata BENAZIR wadda acikinsu itace baa yankawa ragon sunan dayake yankawa sauranba wanda yana yankawa yake siyarda rabi rabin a soya masa yaci abinsa sauran a dan rarrabawa mayun makota masu nacin zuwa idan an haihu din shima hande ce take rabawar sbd itakuma duk wata barna da ‘danta yakeyi tsayawa takeyi ta boye  shiyasa take faran faran da jamaar waje ta yanda babu wanda zai taba sanin halinda Anne da ‘yayanta suke ciki duk da shi rashin gata da rashin kulawar dasuke samu a bayyane yake amma babu me tankawa sbd zafi da tsananin rashin daukan hakuri a lamarinsa.

Duk wanda yasan Ababa da kalmar zafi da masifar son abin duniya zai fara fassara maka shi,
Akan kudi dala babu abinda yake kunya ko wanda yake kunya kai tsaye yake ba kwana kwana ba shakka a takaice zaka iya dorasa a sahun riqaqqun jahilan komai bayan na Nera.

****Ayau sun wayi gari jikin Annensu yayi tsananin tashi ga wani irin zazzabi mai qarfi daya kamata
Kallo daya zakayi mata tausayinta ya kashe jikinka sbd ciwo ne a jikin wanda baya cikakken hayyacinsa,
Bata jin ciwon zazzabi da juyin qwaqwalwar datake samu,ciwo ne a zuciyarta datayi mata wani irin nauyi da sankarewa batajin komai bata gane komai sai fuskar ‘yayanta guda ukun dake gabanta tsananin sonsu na sake toshe kirjinta,

Maqalqale Safnah tayi tareda kafe sauran da ido bata iya cewa komaj sai jijjiga kanta datakeyi da karfi tana murza idanuwata dasukai wani irin ja na azabar ciwon dake cinta amma batasan me zatace ba batama san meyake mata ciwon ba ita.

Wani irin kuka sumayya ta fashe dashi mai ciwo da rashin sauti tana riqo hannuwan Annen datake sake matse safnah da karfi kaman zata illatata,

Safnah ma hawaye takeyi tana hana kukanta sauti kaman sumayya din tanajin zuciyarta na nauyi sbd tasan kila Anne taji a jikinta itama rabuwa zasuyi wata kila ta dawo ta fanshe su da kudi a hannun mahaifin nasu idan har ta tsira wata kila kuma rabuwarsu ce ta har abada bazasu sake haduwaba…wasu hawayen ne masu zafi suka gangaro mata tana kallon Annen wadda  itama ita take kallo amma bata iya magana sbd daman idan abin ya motsa bata iya magana.

Sunkuyar da kai sumayyah tayi tana tsananta kukanta hannuwanta na toshe bakinta ganin hawaye na gangarowa daga jajayen idanuwan Annen,

Benazir datakai hannu ahankali ta share hawayen annen jin tsananin zafinsu yasata fashewa da wani irin kuka mai tsananin ciwo sbd zafinsu ya tabbatar mata da dole a tsananin hali Annensu take amma bata iya fada.

Kukan benazir yasa dukkaninsu sake fashewa da kuka a tare mara sauti hadda Annen data ga ‘yayanta na kuka cikin kunci musamman ganin kukan Benazir yasa kukansu qaruwa dan ba qaramin qunci kesa Benazir din kuka ba.

Sunaji suna gani suka baro Annen a daki tareda safnah dataqi saki suka fara ayyukansu sbd basason Hande tasan jikin annensu ya tashi Ababa na dawowa zata fada masa dan haka suka ringa boye boye dan karta gane.

A dakin kuwa Safnah kai tsaye ta bude baki ta sanar da Annensu tafiya zatayi idan ta mutu kaman Samirah ta yafe mata.

Gabaki daya rikicewa jikin Annen yayi da kalaman safnah wanda ya sata fita hayyaci haukar ta taso tuburan dan haka ta kirawa sun benazir suna zuwa hankalinsu ya tashi take suka daddaureta a dakin suka hanata motsi sbd Hande naji zata kira Ababa a waya
Idan ya taddata a wannan halin a yau zai rabasu da ita
A yanzu da baisan gidan mahaukataba wani gurin zai iya kaiita ya saki tabi duniya ta yanda bazasu taba ganinta ba ko Allah yasa sun tsira a gaba.

Fizge fizge takeyi sosai tana hawayen radadin zuciya duk da tana cikin hali na gushewar hankali radadin uwar da zata rasa yarta cin zuciyarta yakeyi gashi su benazir basusan abinda Safnah din ta fada mata ba jikin nata ya rikice hakan,

Har dare suna cikin tashin hankali da boye boye dan zuwa lokacin har bakinta suka rufe suna kukan wannan azabar ta dauretan da sukayi ba dan ransu ya so ba amma basuda zabin daya wuce hakan tunda suna tsananin son abarsu ko me zata zama.

Safnah kuwa shedan samun damar tsayar mata da zuciya yayi akan Amafani da ciwon Annen ta gudu sbd a yanzu takai gabar da itama ta rasa nata hankalin qwaqwalwarta na gab da juyewar kaman ta Anne koma fiye,

Kusan dukkaninsu idan aka cire Benazir qwaqwalwarsu kaman ta dade ta tabuwa baa ganewa ne sbd basa tareda kowa haka basuda yanci ko na haukar.

Yanda suka rana haka suka ga dare sbd a zaune dukkaninsu suka kwana sbd yanayin jikin Anne daya kasa sauki ko kadan
Duk wani qarfinta ga qare a fizge fizge takai har bata iya motsawa sai hawayen dake bin gefen idanuwanta
Idanuwanta kuwa kaman zasu fado waje tsaban ja da fitowarsu.

Koda sukai sallar Asuba basu saketa ba dan bazata iya sallah ba a halinda take ciki saidai idan tadawo daidai tayi rankon salloli,

Koda suka fito babu mai iya bude idanuwansa har karshe sbd kumburin kuka dan haka duka aikin  sukayi kansu a qasa kada a gane.

ZAFIN KAI page 5 Mamuhgee

Haka suka sake kwana da Anne a hakan babu sauki ko kadan saima galabaituwar datayi ga daurin da sukayi mata yana cin hannuwanta da qafafunta dole suna kallo sbd ba yanda suka iya,

Sumayyah ce ta fara fahimtar Yanda duk suka bar Annen da safnah a daki sai jikin Annen ya tsananta musamman fizge fizgenta gashi duk ta goge gefen fuskarta har jini yakeyi sbd yanda take goga fuskar daga kwancen datake tana buga kanta.

Cikin mamaki da kasa gasgatawa suka tambayeta meyake faruwa duk suka bar anne tareda ita
Bata boye ba ta sanar musu ta fadawa Anne ne zata tafiyarta kaman samirah.

Cikin firgita sumayyah tafara hawaye tana riqo safnah din tace “ me kika yiwa Mahaifiyar data haifeki?
Kinason kasheta ne?
Kinada tinani kuwa?
Wane irin burin guduwa ne ze saika ki ringa cinnawa mahaifiyarki hauka dan kawai ki gudu.

Benazir fararen idanuwanta dasukai laushi da galabaita ta zubawa Anne dake sake goge fuskarta da qasa batareda da jin zafin ciwon data yiwa fuskartata ba,
Sarewa qafafuwanta sukayi tanajin kaman zata gaza,
Itama taya qwaqwalwar jin tayi kaman zata buga dan lamarinsu na gab da qarasa tabarbarewa idan suka fara samun son kai da rashin tausayin juna a tsakaninsu.

Safnah da zuciyarta tafara bushewa ta kallesu tasake tabbatar musu da guduwa zatayi ta zabi bin duniya akan zama karkashin Ababa.

Sumayyah kuka kawai takeyi tana kokarin dawo da tinanin safnah din a hanya amma sam safnah taki sauraranta sai hayaniya taso barkewa tsakaninsu
Benazir data rasa abin fada ko yi sai kawai ta qarasa gurin Anne ta dagota zaune ta kwantar da kanta a jikinta tana goge mata jinin fuskarya da hannun zumbuleliyar doguwar rigar gwanjon dake jikinta sbd sune suturarsu.

Sumayyah da duk ta firgice da tashin hankali da tsoron jin kudirin Safnah din kallon Benazir tayi cikin tsoron abinda zai iya biyowa baya tace

“Benazir kiyi mata magana dan Allah kada ta aikata hakan”

Rintse idanuwa Benazir tayi tareda yiwa safnah din kallo daya wadda ke kallonta itama kaman suna yiwa juna kallon dayake faduwar da gabansu su duka biyun saidai kowannensu ya kasa furta kalma ko daya.
Daga hakan dakin ya dauki shiru sai hawayen sumayyah dake zuba tana fidda karamin sautin kuka.

Da daddare duk fada da yada maganganun Hande akan rashin fitowar Anne basu ce komaiba sbd kada ta tsananta tace sai Annen ta fito.

Safnah bata saduda ba cikin kwana biyu ta tabbatarda ta zaburar da ciwon Anne gabaki daya ta hanyar dawo mata da yanda Samirah ta rasu da yanda itama zata tafi ta barta,
Babu mai imanin da zai kalli Annen bai zubar mata da hawaye ba hakama su benazir sun shiga mawuyaci matsanancin hali na yanayin mahaifiyarsu haka Safnah kusan takoma tamkar maqiyarsu sbd yanda ta fidda asalin son kanta da tsame kanta daga halinda Annensu take ciki gashi basuda ikon hayaniyar da zata ankarar dasu Hande halinda suke ciki dan haka suka zabi tattarawa su koma bangaren dabbobi sbd tsanani da lamarin ya qara.

A ranar da sukai kwana biyar a wannan halin da rana tsaka Suna can suna aikin wankin kayan Ababa dana Hande ga aikin wankin fatar da aka kawo kusan mota biyu sunata yi cikin gajiya da yunwa.

Safnah silalewa tayi ta koma dakin dasuka rufe Annen ta tsaya a kanta tana kallonta tsawon mintina kafin ta sauke numfashi mai zafi ta durkusa ta warware mata daurin da sukai mata na hannuwa dana kafa.

Sanin da rana Ababa baya gida Hande ce take tsaronsu ko ina bata zuwa sbd su din haka koma ta fita tabar musu gidan a bude Annensu bazata taba iya guduwa tabar gidanba sbd aikin da Ababan yayi mata daga ranar daya aureta duk tsanani da azaba bazata iya tafiyaba har sai ranar daya gaji yace ta tafi da kansa.

Janyo Annen tayi ta nuna mata dakin Hande tace mata taje can samirah na ciki Hande ta boye.

Jin hakan yasa Anne da qafafuwanta duk sukai sanyin dauri amma bata damuba sbd ciwo ta nufi dakin Hande da gudu ta fada tana zubar da kaya tana neman samirah idanuwanta a waje bata ji bata gani.

Cikin bacci hande taji kaya tako ina a kanta a firgice ta tashi tana neman dauki sbd komai janyowa Annen keyi ta yadda ta fasa tana neman ‘yarta.

A rikice zani na neman sauka Hande ta fito tana ihu tana neman agaji saidai su benazir na can gangaren dabboni basa ji sosai
Safnah dake boye tana jiran hande ta bude gida ta sake leqowa zuciyarta na wani irin tsalle da azababben tsoron yaya tata qaddarar guduwar zaya qare.

Kan Hande dake daura zani Anne tayi tana kokarin duba ‘yarta cikin zanin
Tini hande tayi hanyar kofar gida tana fizgo dankwalin kanta sa mukullan gidan ke ciki daure ta bude gidan da sauri hannuwanta na rawa dan a duniya tana tsoron mahaukata tunda sukai sanadiyar rasa hakorinta biyu  a wani kauye dataje biki.

Tana bude gidan ta fice da sauri tayi bayan gidan tana kwada kiransu Benazir dake ta cikin gidan hankali tashe dan bazata shigoba sai sun kama uwarsu sun daure.

Safnah dataji wani nannauyan abu ya fada daga kan kirjinta bayan ficewar hande fitowa tayi daga mabiyarta ta mufi kofar gidan batareda ko so daya ta waiwaya ta kalli inda mahaifiyarta ta fadi qasaba tana buga kanta sa qasa ta fice daga gidan ta bi ta bayan da Baa nan Hande takeba ta lullube kanta ruf da qaton mayafin Hande data dauka a igiyar shanya ta dosa daji kai tsaye sbd idan ta nufi cikin gari zata dade bata bar garin ba.

Su Benazir dake galabaice suna aiki ba wani qwari ko cikakken kuzari a jikinsu sukaji ihun kiran da Hande ke musu ta katangar bayan gidan da sauri suka taso hankalinsu tashe.

Benazir ce tayi kan Anne da gudu tana riqeta daga ciwon datake jiwa kanta,

Sumayyah kuwa tsaban rikicewa da firgici ‘dakin handen ta nufa tafara tattarawa babu inda baya rawa a jikinta cikin mintina kadan ta gyare dakin ta maida komai inda yake ta fito har lokacin a rikice take dan tasan yau suda mahaifiyarsu sai Allah.

Benazir kuwa cikin matsanancin tashin hankali take jan Annen takaita daki ta fashe da kuka mai qarfinda bata taba sakiba a rayuwarta.

Kukan Benazir yasa Anne tsayawa cak daga mutsu mutsun datakeyi ta zubawa Benazir din ido kaman me nazari.

Kuka sosai Benazir keyi tana sarewa daga komai na rayuwa,
Sumayyah na shigowa a firgice sunan safnah tafara kira tana cewa,

“Ina safnah?
Ina tayi?
Bangantaba?
Bata koina…

Dakin tabi da kallo bataga safnah din ba qarin sautin kukan Benazir ya tabbatar mata da safnah ta tafiyarta kuma tabbas itace ta warware Anne ta sakota,
Kenan da mahaifiyarsu tayi amfani dan cimma burinta a mafi wulaqancin hanya tayi amfani da uwar data haifeta.

Silalewa itama tayi qasa ta fasa kuka mara sauti dan batada karfin yin me sautin ma koda taso.

Wani irin kuka sukeyi wanda radadinsa ke fitowa daga qarqashin qasan rai mai ciwo da qunci da baqin ciki tareda qaqa nikayi.

Kaman an yayyafawa wuta ruwa ta mutu haka Kukansu ya yayyafawa yanayin Annensu sanyi gabaki daya ta rakube guri daya tayi shiru tana kallonsu da idanuwanta dasu kansu ciwo sukeyi na rashin bacci da zarewa.

Lokaci mai tsayi suka dauka a hakan kafin suka fito sukai Alwalan sallar magriba suka dawo sukayi kafin suka kama Annen suka fito da ita zuwa can bayin baya da akai musu a cikin dabbobi sukai zaunar da ita kan kujerar karfe sukai mata wanka fes sbd tunda tafara ciwon bata samu wanka ba.

Kaman yarinya qarama haka suka kamota suka dawo da ita abincin da Hande ta basu cin mutum daya shi suka barwa Annen tacinye rabi rabin duk ya zube.

Shiru sukayi a daki babu me iya magana sbd rashin sanin makomarsu data Annensu suna jiran dawowar Ababa.

Addua sukaita tofawa Annensu suna rokon Allah sauki da mafita sai gashi cikin yardar Allah bacci ya dauketa a inda take zaune dan haka suka gyara mata kwanciya tareda rufeta da wani barkakken zani.

Guraren karfe tara sukaji bude kofar gidan a tare dukkaninsu suka miqe daga kwancen da suke jikin sumayyah na wani irin kerma da fizga ta kalli benazir wadda su kadai suka ragewa juna gashi benazir nada juriya da jarumta amma sam ita Allah bai bata ko daya ba sbd kusan rauninta yafi na kowannensu.

Ahanakali Benazir ta tashi tsaye tareda kama sumayyah din da bazata iya miqewa ba sbd tsananin kerma da tsallen da zuciyarta keyi kaman zata buga.

Kafafuwansu na rawa suka fito tsakar gidan da tini Hande tafara zayyane masa abinda ya faru.

Tsayawa sukayi daga inda sukasan yana basu umarnin nesancinsa dasu.

Wani wulaqantaccen kallo yake musu kowaccensu kanta na qasa suna kokawa da tarin tsoron dake zuciyoyinsu.

Ganin su biyu kawai yasashi juyowa da kyau yana kallonsu babu alamar rahamar kauna ko tausayi na digo daya a fuskarsa da Amon muryarsa me gigita duk wani ruwa da abinda yake aiki a jikinsu kai tsaye yace,

“Ina Safnah?”

Wani qarar kuka mai qarfin gaske ne ya fito daga cikin Sumayyah datake gab da shidewa sbd tashin hankali.

Idan yana tsaye sumayyah bata taba iya magana sbd firgita dan haka Benazir da itama take cikin mawuyacin halin tashin hankali dole tayi qarfin halin bude baki muryarta na wata irin rawa tace,

“Bata nan ta tafi……..Wani jahilin marin bayan hannu ya saukar mata ba zata a fuska wanda yasata kifewa a gurin bakinta na fashewa.

Tasowa tayi batareda ta dora hannu a gurin ba still kanta na soke a qasa dan basa dagowa a gabansa.

Shaqota yayi idanuwansa waje take wani kumfa na tsananin masifa ya cika bakinsa yana fesowa ya sake sauke mata wasu marikan guda uku a jere yace,

“Bata nan ina taje??

Duk wuya baya tambaya aqi amsawa dan haka cikin azaba tace,

“Ta gudu”
Wurgi yayi da ita dukkanin jikinsa na rawar masifa da tsananin bacin rai na wutar masifa dake babbaka jininsa ya shaqo sumayyah wadda takusa sumewa dan numfashinta iya wuyanta yake tsayawa baya kaiwa cikinta sbd ganin tashin masifarsa.

KARANTA: Amfanin Kanunfari ga Maza da Mata